Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bukaci majalisar tarayya da ta binciki tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta ba hukumar NAHCON domin hajjin bana.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi zargin cewa wasu daga cikin 'yan majalisar tarayya a jihar na adawa da shirye-shiryen ci gaba da yake da su.
Dakarun sojojin sama sun yi nasarar lalata haramtattun wuraren tace man fetur a jihohin Imo, Rivers da Bayelsa. Sun kuma lalata kayayyakin da ake amfani da su.
Shugaban cocin Christ Embassy, Fasto Chris Oyakhilome ya yi magana kan gobarar da ta tashi a hedikwatar cocin da ke Legas. Faston ya ce za su sake gina babba.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da wani jami'in 'yan sanda da direban wani babban basarake a jihar Rivers bayan sun kai farmaki a fadarsa.
Shugaban kasan Bola Ahmed Tinubu, ya yi umarni da a hukunta ma'aikatan da suke karbar albashi a kasar nan duk da cewa sun koma kasashen waje da zama.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga jami'an tsaro da su dauki mataki mai tsauri kan 'yan daba masu tayar da rigima a cikin birnin Kano.
Rahotanni sun ce wasu da ake zargin sojojin ruwa ne sun hallaka wani dan sanda a birnin Legas. Lamarin ya auku ne dai bayan gardama ta barke a tsakaninsu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari