Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi martani ga Sanata Ali Ndume kan sukar da ya yiwa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. APC ta ja masa kunne.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana harin kunar bakin wake da 'yan ta'adda suka kai a jihar a matsayin kokarin yiwa gwamnatinsa zagon kasa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa. Shugaban kasan ya nada sabon shugaban hukumar CCT da wasu hukumomi shida.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim, ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tare da jiga-jigan 'yan adawa a Ebonyi.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kubutar da wasu mutum 57 da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace a dajin Sambisa. Sojojin sun kuma hallaka 'yan ta'adda.
Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Sanata Sunday Karimi ya gargadi takwaransa, Sanata Ali Ndume kan sukar gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kara yawan majalisar zartaswar jihar. Gwamnan ya rantsar da sababbin kwamishinoni guda biyu da wasu hadimai.
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a shirye yake ya kawo karshen matsalar tabarbarewar tattalin arziki.
Wani ginin bene mai yawa biyu ya rufto a birnin tarayya Abuja. Ginin ya rufto a kan mutane masu yawa. Mutane da yawa sun makale yayin da aka fara aikin ceto su.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari