Manyan Labarai A Yau
Babban jigo a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Uche Nwosu, ya bukaci 'yan Najeriya da su hakura da zanga-zangar da suke shirin yi a fadin kasar nan.
An samu asarar rayukan mutum hudu bayan wani gini ya rufto musu a jihar Legas. Hukumomi sun samu nasarar ceto mutum biyar da lamarin ya ritsa da su.
Gwamnatin jihar Bauchi ta fito ta bayyana cewa babu wata zanga-zangar da za a gudanar a fadin jihar. Ta gargadi masu shirin yi da su tafi wani waje ba Bauchi ba.
Kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya ta bayyana cewa ofishin NSA zai taimakawa gwamnoni wajen kara inganta tsaro yayin da ake shirin yin zanga zanga.
Marasa rinjaye na majalisar wakilai sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tattauna da masu shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta gayyaci shugabanninta na jihohi 36 ma kasar nan zuwa taro kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga watan Agusta.
Rahotanni daga jihar Osun sun tabbatar da cewa an yi asarar rayuka biyu a rikicin da ya ɓarke kan sarauta a yankin ƙaramar hukumar Ayedaade ranar Talata.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ko kadan bata son matasa su gudanar d azanga-zanga a fadin kasar nan, saboda wasu za su iya tayar da rikici a kasa.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga masu shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan da su kwantar da hankulansu. Gwamnatin ta ce a kara mata lokaci.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari