Manyan Labarai A Yau
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan shirin hana 'yan kasa yin zanga-zanga.
Babban Sufeto-Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ja kunnen masu fakewa da zanga-zanga domin tayar da rikici a fadin kasar nan.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin sabon mafi karancin albashin ma'aikata wanda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya mika a gabanta.
Yusuf Adamu Gadgi na wakiltar mazabar Pankshin/Kanam/Kanke a majalisar wakilai a karkashin inuwar jam'iyyar APC. Ya taba rike mukamin mataimakin kakakin majalisa.
Sanatan Najeriya daga jihar Anambara ya bukaci a canza tsarin zaman majalisa saboda kudin da ake biyansu ya yi kadan kuma suna zama sosai suna shan wahala.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kan jami'an 'yan sanda da ke aikin sintiri a jihar Abia. Miyagun sun hallaka Sufeton 'yan sanda da wasu mutum uku.
Majalisar wakilai ta dauki matakin shawo kan rikicin da ya barke tsakanin Aliko Dangote da gwamnatin Tinubu wanda hukumar NMDPRA ta koka kan matatar Dangote.
Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta yi babban kamu bayan daruruwan mambobin jam'iyyun adawa na PDP, APGA da LP sun dawo cikinta. Sun sha alwashin ba da gudunmawarsu.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kakaba sabon harajin N425bn kan wasu bankuna guda bakwai saboda ribar da suka samu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari