Manyan Labarai A Yau
Kungiyar SERAP ta shigar da kara kan gaza bayani inda yagaggun kudi na N100bn suka yi. SERAP na kuma karar bankin kan wasu zarge-zarge guda biyu.
'Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai farmaki a wani ofishin 'yan sanda da ke jihar. Sun hallaka mutum tare da kona motoci da babura.
Gwamnatin jihar Plateau ta fito ta yi martani kan zargin cewa ta ware N3.9bn domin siyo motocin alfarma ga gwamnan jihar. Ta fadi yadda abin yake.
Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a iyakokin kasar nan. Hukumar kula da shiga da fice ta umarci jami'anta da su sanya idanu sosai a lokacin zanga-zanga.
'Yan majalisar dokokin jihar Kebbi guda uku da aka zaba a inuwar jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar. Sun samu tarba mai kyau.
Kungiyar 'yan asalin jihar Zamfara ta fasa shiga zanga-zangar da za a yi a fadin kasar nan a ranar 1 ga watan Agustan 2024. Ta ce babu tsari mai kyau.
An kawo maku sunayen 'yan majalisar tarayyar da mutuwa ta raba da mazabunsu. A ciki akwai Ifeanyi Uba wanda Sanata ne da Isa Dogonyaro da Abdulkadir Jelani Danbuga.
Tsohon shugaban kasan Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa za a yi yaki idan bai lashe zaben shugaban kasa ba da za a gudanar a watan Nuwamban 2024.
Ministan albarkatun ruwa, Muhammad Goronyo ya bukaci 'yan Najeriya da kada su shiga cikin zanga-zangar da ake shirin yi domin adawa da gwamnatin Bola Tinubu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari