Manyan Labarai A Yau
Muhammad Ali Ndume ya ƙi karban sabon ofishin da aka ba shi a majalisar dattawa bayan sauke shi daga matsayin mai tsawatarwa saboda ya soki Bola Tinubu.
Matasa a Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen fitowa domin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan. Zanga-zangar za a yi ta ne saboda tsadar rayuwa da talauci.
Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Dauda Lawal ta amince da ba da aikin titin hanyar Magami zuwa Dansadau wanda zai lakume makudan kudade har N81bn.
Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su bude layukan da suka rufe saboda rashin sanya lambar NIN. Ta ja kunnen kwastomomi.
Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun fara rufe layukan wayoyi wadanda ba a sanya musu lambar NIN ba. Ga hanyoyin yadda ake bude layin MTN da aka rufe.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram a jihar Borno. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda takwas.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a sansanin jami'an hukumar kwastam a jihar Kebbi. Sun hallaka jami'i daya tare da sace wani jami'in.
Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo ya bukaci 'yan Najeriya da su kara ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu lokaci ya magance matsalolin kasar nan.
Kungiyar Arewa Youth Assembly, ta ba shugaban matatar man Dangote shawara kan rikicinsa da hukumomi a Najeriya. Kungiyar ta ce ya bi doka kawai ya huta.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari