Manyan Labarai A Yau
Babban sufetan ƴan sanda na ƙasa IGP Kayode ya ce rundunar ƴan sanda ba za ta zuba ido tana kallo wasu su tayar da tarzoma a ƙasar nan da sunan zanga zanga ba.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Edo, Funsho Adegboye, ya bayyana cewa za su goyi bayan masu gudanar da zanga-zanga a jihar. Ya kafa musu muhimmin sharadi.
Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakin rufe makarantu saboda zanga-zangar da za a fara gudanarwa a fadin kasar nan kan tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Agusta.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna goyon bayansa kan zanga-znaahr da matasa ke shirin fara gudanarwa a fadin kasar nan daga ranar 1 ba watan Agusta.
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci 'yan Najeriya da su kara ba shugaban kasa Bola Tinubu lokaci. Godswill Akpabio ne ya yi wannan rokon a Abuja.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, ta sanya lokacin da za ta gudanar da zabe a kananan hukumomi 44 na jihar. Ta kafa sharudda ga 'yan takara.
Kungiyoyin matasa, dalibai da nakasassu a jihar Kwara sun fasa shiga zanga-zanaga da aka shirya gudanarwa a fadin kasar nan daga ranar 1 ga watan Agusta.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yiwa jami'an rundunar tsaron jihar Sokoto kwanton bauna. 'Yan bindigan sun hallaka mutum biyar tare da wasu manoma.
Majalisar dattawa ta nemi jin ba'asin kan kudaden da aka ware a kamfanin tama da karafa na Ajaokuta a cikin kasafin kudin 2024 duk da cewa kamfanin ba ya aiki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari