Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin Najeriya ta bukaci al'ummar Najeriya da ke Birtaniya da su yi taka tsantsan kan shiga taruka da zanga zanga bayan an fara zanga zanga a Birtaniya.
Dan majalisar da ke wakiltar Doguwa/Tudun Wada a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya caccaki takwaransa na jam'iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin Kofa.
Jami'an tsaro sun dira a kan mutanen da suka fito zanga-zangar nuna adawa da halin kuncin da ake ciki a kasar nan. Sun cafke mutum uku a birnin Abuja.
Jigon jam'iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci a dora alhakin barnar da aka yi a Kano yayin zanga-zanga kan Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang, ya sanya dokar hana fita bayan wasu bata gari sun yi sace-sace a shagunan mutane yayin zanga-zanga a jihar.
Tsohon shugaban kasan Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya musanta cewa ya fi son mulkin soja fiye da na dimokuradiyya a kasar nan.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ja kunnen matasan Najeriya da kada su bari a yi amfani da su domin kawo cikas ga mulkin dimojuradiyyar kasar nan.
Gamayyar wasu kungiyoyin farar hula a jihar Katsina sun caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan jawabin da ya yi dangane da zanga-zangar da ake yi a kasa.
Wasu 'yan daba sun tafka barna a coci bayan sun kai farmaki yayin da ake zanga-zanga a jihar Katsina. 'Yan daban sun kwashe kayan miliyoyin naira.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari