Manyan Labarai A Yau
Wani babban mamba a jam'iyyar PDP ya bukaci shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya yi murabus ya hakura da jagorancin kamfanin.
Tsohon mai binciken kudi na kasa na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Cif George Moghalu, ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar. Ya fadi dalilinsa.
Tsohon dan majalisar wakilai, Honorabul Lanre Laoshe, ya biya gwamnati rancen kdin karatu da aka ba shi lokacin da yake karatunsa. Ya nuna godiyarsa.
Miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a jihar Nasarawa. 'Yan bindigan sun hallaka mutum daya tare da sace wasu mutum biyu a yayin harin da suka kai.
Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya gatgaɗi shugabannin Afirka da su tashi tsaye su tunkari ƙalubalen da suka addabi matasa tun kafin lokaci ya ƙure.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun hallaka yaron babban basarake a jihar Legas. 'Yan bindigan sun hallaka yaron basaraken ne mai sarautar Ojomu na Ajiran a Legas.
Rikicin shugabanci ta taso jam'iyyar APC a gaba a jihar Enugu. Tsagin da ke samun goyon bayan shugaban jam'iyyar na kasa, ya dakatar da mambobi 20.
Dakarun sojohin Najeriya sun samu nasara kan miyagun 'yan ta'addan da ke aikata ta'addanci a jihar Kaduna. Sojojin sun kwato makamai masu tarin yawa.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami, ya yi magana kan hanyar kawo karshen 'yan bindiga da sauran matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari