Manyan Labarai A Yau
Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta yi Allah wadai da harin da 'yan ta'adda suka kai a jihar Yobe wanda ya yi sanadiyyar hallaka rayukan mutane masu yawa.
Majalisar sarakunan gargajiya na Kudancin Najeriya ta yi Allah wadai kan kisan gillar da miyagun 'yan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa.
Wata kotun majistare da ke a birnin Kano ta ba da belin wani dan jarida da aka tsare a gidan gyaran hali kan zargin sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanusi II.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a sakatariyar karamar hukumar Isiala Mbano da ke jihar Imo. 'Yan bindigan sun hallaka jami'an tsaro a yayin harin.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sha alwashin kare mutanen jihar daga barazanar rashin tsaron da suke fuskanta daga wajen 'yan bindiga.
Kungiyar NCYP ta ba gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani shawara kan ya guji maimaita irin kura kuran da magabacinsa, Nasir Ahmad El Rufai ya yi.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi martani kan karin kudin man fetir da aka yi a kasar nan. Kungiyar ta ce shugaban kasa Bola Tinubu ya yaudare ta.
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun fusata kan kalaman da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi. Sun bukaci jami'an tsaro su zama cikin shiri.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya shawarci kwamishinan 'yan sandan jihar da sauran jami'an rundunar da su guji sanya siyasa a cikin aikinsu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari