Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin tarayya ta fito ta yi magana kan dalilin da ya sanya jami'an tsaro suka cafke shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sun kara tabarbarar da tattalin arzikin kasar nan. Ta fadi dalili.
Wasu jihohi a Najeriya sun dauki matakin dage ranakun da dalibai za su koma makarantu. Wasu daga ciki sun dauki matakin ne saboda tsadar fetur da wasu dalilan.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya yaba da matakin da matasan jihar suka dauka na kin shiga zanga zangar da aka yi a kasar nan. Ya ba su kyautar N310m.
An samu asarar rayukan mutum uku bayan wani gini ya rufto a jihar Jigawa. Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar ceto mutanen da ginin ya rufto a kansu.
Sanata Ali Ndume ya nuna alhininsa kan ambaliyar ruwan da ta auku a birnin Maiduguri na jihar Borno. Sanatan ya bukaci gwamnatin tarayya ta kai dauki a jihar.
Babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Christopher Musa ya sha alwashin cafke kasurgumin shugaban 'yan bindiga, Bello Turji nan da dan kankanin lokaci.
Mahukuntan jami'ar Borno (UNIMAID) sun dauki matakin rufe jami'ar har sai abin da hali ya yi sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a birnin Maidiguri na jihar.
A wannan labarin, daurarrun da ba a kai ga sanin adadinsu ba sun samu damar tserewa daga kurkukun da aka ajiye su bisa laifuffuka daban-daban a Borno.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari