Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matatar man Dangote za ta fira fitar da man fetur daga ranar Lahadi. Gwamnatin ta ce kamfanin NNPCL kadai za a ba fetur.
Tafiye tafiyen da uwargidan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Remi Tinubu ta yi zuwa kasashen waje sun lakume kudade masu yawa. Gwamnati ta kashe N700m.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sake fitowa ya nuna yatsa ga gwamnonin jam'iyyar PDP. Wike ya ce bai ci amanar jam'iyyar ba.
Gwamnatin Najeriya ta kashe N26m domin aikin gyaran madatsar Alau a ranar 29 ga watan Yulin 2024, kusan wata daya kafin ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri.
Gwamnan jihar Jigawa, Ahmed Umar Namadi ya kaddamar da shirin rabon kayayyakin tallafi ga mutanen da bala'in ambaliyar ruwa ta ritsa da su a jihar.
Jami'an runduna tsaron farin kaya DSS da ƴan sanda sun karɓe iko da fadat Ilesa bayan an fara yaɗa jita-jitar Allah ya yiwa mai martaba sarki, Oba Aromolaran rasuwa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tare babban titin hanyar Gusau zuwa Funtua a jihar Zamfara. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da matafiya masu dumbin yawa.
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sabuwar ranar da dalibai za su koma makarantun firamare da na gaba da firamare a fadin jihar. Za a koma a cikin watan Satumba.
Kotun daukaka ta zartar da hukunci kan karar da ke neman soke tikitin takarar gwamna na Barista Olumide Akpata karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari