Manyan Labarai A Yau
Mazauna unguwar Mpape, da ke a karamar hukumar Bwari a cikin babban birnin tarayya |Abuja sun shiga cikin firgici sakamakon wata girgizar kasa da aka yi.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi magana kan hatsarin jirgin ruwan da ya auku a jihar wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutane 40.
Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya bayyana farashin da zai sayar da fetur wanda ya samu daga matatar Dangote da ke a jihar Legas. Farashin na watan Satumba ne.
Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta ba ma'aikatan jihar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW).
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ba da gudunmawa ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno. Atiku ya ba da N100m.
Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda ta amince da fitar da N340m domin gyara wutar lantarkin jami'ar UMYUK wacce ta lalace.
Jami'an tsaro na hukumar shige da fice ta Najeriya sun saki Omoyele Sowore jim kadan bayan sun cafke shi bayan ya dawo daga kasar Amurka a ranar Lahadi.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a jihar Enugu inda suka tafka ta'asa. 'Yan bindigan sun hallaka wani shugaban 'yan kasuwa a jihar bayan sun kai masa farmaki.
Ambaliyar ruwa ta raba mutane fiye da miliyan daya da muhallansu a Maiduguri da kewaye. Majalisar Dinkin Duniya za ta kai daukin abinci da samar da matsugunni.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari