Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Sokoto ta bayyana cewa a shirye take kan binciken da ake yi bisa zargin karkatar da N16bn da ake yiwa Aminu Waziri Tambuwal.
Uwargidan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu ta ba da gudunmawar N500m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ja kunnen sarakunan Borno kan illar da ke tattare da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a jihar.
Wata kungiyar dattawan jihar Zamfara ta shawarci gwamnan jihar Dauda Lawal da ya mayar da hankali wajen sauke nauyin da ke kansa maimakon sukar Bello Matawalle.
Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ba mika wuya ya yi ba. Ta ce cafke shi aka yi.
Kungiyar 'yan majalisar wakilai marasa rinjaye ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rage farashin fetur. Kungiyar ta ce tsadar ta yi yawa duba da halin da ake ciki.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya amince zai amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa kan zargin karkatar da makudan kudaden da suka kai N80.2bn.
Tsohon jigo a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Salihu Lukman ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Ya ce shugaban kasan bai bari ana ganinsa.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ba da gudunmawar Naira miliyan 20 ga iyalan mutanen da mummunan hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da su a jihar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari