Manyan Labarai A Yau
An kama mutane uku da zargin kitsa juyin mulki ga shugaban kasar Benin. An kama kwamandan sojoji, ministan wasanni da wani babban dan kasuwa a kasar.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun mininstan shari'a, Lateef Fagbemi ta musanta batun cewa wata kotu ta umarci a kwace kudadenta a kasar Amurka.
Kungiyar NYA ta fito ta yi magana kan rikicin da ake yi tsakanin gwamnan Zamfara da Bello Matawalle. Kungiyar ta ce Dauda Lawal na tsoron ministan na Tinubu.
Jam'iyyar APGA ta fara aiwatar da shirye-shiryen dakatar da gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo. Jam'iyyar APGA na zarginsa da yi mata zagon kasa.
Rabaran Gabriel Abegunrin ya ba gwamnatin tarayya shawara kan yadda fetur zai yi arha. malamin addinin ya bukaci a bar Dangote ya sayar da fetur ga 'yan kasuwa.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya kare matakin da ya dauka na yin sulhu da 'yan bindiga a lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar Zamfara.
Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta yi barazanar shiga yajin aiki. Shugaaban ASUU ya ba gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 kan lamarin.
Gwamnatin jihar Bauchi ta gabatar da karin kasafin kudi a gaban majalisar dokokin jihar domin neman ta amince da shi. Za a yi ayyuka masu muhimmanci a cikinsa.
Babban hafsan sojojin kasan Najeriya (COAS), Taoreed Lagbaja, ya koka kan karancin jami'an tsaron da ake da su a kasar nan. Ya ce ba za su iya kare 'yan Najeriya ba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari