Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana kan matsalolin da suka addabi kasar nan. Gwamnan ya ce gwamnati na aiki tukuru domin magance su.
Kungiyar Arewa Peace Foundation (APF) ta fito ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal. Ta bukaci mutanen Zamfara su ba shi hadin kai.
Dan majalisar dokokin jihar Cross Rivers na jam'iyyar Labour Party (LP) ya fice saga jam'iyyar zuwa APC mai mulki. Ya samu tarba daga jiga-jigan APC a jihar.
Jami'an tsaro sun samun gagarumar nasara kan 'yan bindiga a jihar Katsina. Jami'an tsaron sun yi nasarar kubutar da manoma shida da aka yi garkuwa da su.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin bikin murnar cikar Najeriya shekara 64 da samun 'yancin kai.
Darajar Naira ta ci gaba da yin raga raga a kasuwar canji. Naira ta yi faduwar da ba ta taba yin ba a cikin watanni bakwai. Farashin Dala ya ci gaba da tashi.
Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, ya yi Allah wadai da kalaman da Gwamna Dauda Lawal yake yi kan karamin ministan tsaro Bello Matawalle.
Ba tsadar Allah da Annabi ake samu a kasuwa ba, Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu ya nuna akwai hannun wasu mugayen 'yan kasuwan da ke Najeriya.
Matar gwamnan jihar Akwa Ibom ta rasu. Legit ta tattaro muku abubuwa 5 masu muhimmanci kan matar gwamnan da ta rasu bayan rashin lafiya a asibitin Najeriya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari