Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar APC ta samu tagomashi bayan dan majalisar wakilai na PDP ya sauya sheka zuwa cikinta. Dan majalisar na PDP dai ya fito ne daga jihar Abia.
Jam'iyyar APC ta samu koma baya a jihar Ondo bayan mambobinta sama da 200 sun sauya sheka zuwa PDP. Sun fadi dalilinsu na ficewa daga jam'iyyar mai mulki.
A shekarar 2006 aka yi yaki tsakanin Hisbullah da ksar Isra'ila. Hisbullah ta samu nasara a kan Isra'ila inda ta kashe sojoji kimanin 121 da lalata motocin yaki.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi magana kan matsalolin da suka yiwa jam'iyyar PDP katutu a kasar nan. Gwamnan ya bukaci a daina kalamai masu kaushi.
Iran ta kai hare haren Isra'ila a ranar Talata. Harin da Iran ta kai Isra'ila ya biyo bayan kashe shugaban Hamas da Hisbullah ne da Isra'ila ta yi a kwankin baya.
Kungiyar Mandate Protection Vanguard (MPV) ta ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan mutanen da ya kamata ya nada a matsayim ministoci a gwamnatinsa.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ko kadan ba zai yi ritaya daga siyasa. El- Rufai ya ce zai dawo a shekarar 2027.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutanen da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su a jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.
Al'ummar jihar Kaduna ba su fito zanga zangar #October1Fearless da aka shirya gudanarwa a fadin Najeriya ba. Mutane sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari