Manyan Labarai A Yau
Wasu miyagun ƴan bindiga dauke da makamai sun kai hari a garin Kachia da ke juhar Kaduna. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da shugaban makaranta a harin.
Ministar al'adu da tattalin arzikin fikira, Hannatu Musa Musawa ta bayyana cewa ba ta damu da shirin sauya wasu ministoci da Shugaba Bola Tinubu ke shirin yi ba.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a jihar Kebbi. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da Hakimin Kanya tare da wasu mutane da dama a harin na ranar Asabar.
Hukumar masu yi wa kasa hidima ta Najeriya (NYSC) ta bayyana cewa ta samu jinkiri ne wajen fara biyan masu yi wa kasa hidima sabon alawus saboda babu kudi.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bukaci shugabanni su hada kai domin ceto kasar nan daga halin da ta tsinci kanta a ciki a yanzu.
Shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa nan gaba kadan 'yan Najeriya za su fito su rika gode masa kan matakan da ya dauka a kasar nan.
An samu tashin gobara a babbar kasuwar Kantin Kwari da ke jihar Kano a daren ranar Asabar. Gobarar wacce ta tashi, ta lakume shaguna masu yawa a kasuwar.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ba ma'aikatan gwamnatin jihar tabbacin ceqa zai fara biyan mafi karancin albashi na N70,000 nan ba da jimawa ba.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bukaci da ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya shigar a gabanta.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari