Ana Cikin Tsadar Rayuwa Tinubu Ya Fadi Lokacin da 'Yan Najeriya Za Su Gode Masa
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matakai masu tsauri da ya ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan
- Shugaba Tinubu ya ce lokaci zai zo wanda ƴan Najeriya za su yaba masa saboda ɗaukar waɗannan matakan
- Ya bayyana cewa wajibi ne a ɗauki matakan domin dawo da ƙasar nan a kan turbar da ta dace saboda samun ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaba Bola Tinubu ya ce lokaci na zuwa da ƴan Najeriya za su yaba kan yadda gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu tsauri.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin babban taron jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Yamma a otal ɗin Eko da ke Legas.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar da suka haɗa da gwamnoni, mataimakan gwamnoni, ƴan majalisar tarayya da na jihohi, da kuma tsofaffin shugabanni, cewar rahoton jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu na sane da halin da ake ciki
Jaridar TheCable ta ce da yake jawabi a wajen taron, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, wanda ya wakilci Tinubu, ya ce sauye-sauyen da gwamnati mai ci ta ɓullo da su sun janyo suka ga jam’iyyar.
Ya kuma tabbatarwa da ƴaƴan jam’iyyar ta APC cewa tsauraran matakan da ya ɗauka za su ɗora ƙasar nan kan turba, ya kuma ƙara da cewa ya yaba da irin goyon bayan da ake ba gwamnatinsa.
"Mun yarda cewa matakan da muka ɗauka sun yi tsauri, amma akwai buƙatar mu ɗauke su. Za a ga amfanin hakan a nan gaba.
"Wannan lokacin zai zo wanda za mu yi farin ciki mu godewa gwamnati bisa ɗaukar waɗannan matakan."
"Wannan ne ya sa muke aiwatar da gyare-gyaren da aka daɗe ba a yi ba. Wannan ita ce alamar shugaba na gari."
- Bola Tinubu
Tinubu ya magantu kan zaɓen 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zaɓen shekarar 2027 da ake ta shirye-shirye.
Shugaba Tinubu ya ce a yanzu ko kadan bai damu da zaɓen 2027 ba saboda ya maida hankali wajen nemo hanyar kawo sauyi ga ƴan Najeriya.
Asali: Legit.ng