Manyan Labarai A Yau
Uwargidan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Remi Tinubu ta mika sakon ta'aziyya kan mutanen da suka rasu sakamakon fashewar tankar man fetur Jigawa.
Shugabannin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun sanya labule da gwamnatin tarayya. Ganawar na zuwa ne bayan an kara farashin man fetur a kasar nan.
Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta koka kan rashin kudin da take fuskanta a ma'aikatarta. Ta bayyana cewa da kanta take daukar nauyin wasu ayyukan.
Gwamnatin jihar Sokoto ta shirya kaddamar da shirin sayar da shinkafa da sauran kayan abinci bisa farashi mai rahusa. Za a siyar da kayayyaki a mazabun jihar.
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), ya fito ya musanta cimma yarjejeniya da kungiyar dillalan mai ta Najeriya (IPMAN) kan farashin man fetur.
An samu asarar rayuka bayan wata tankar mai ta gamu da hatsari a jihar Jigawa. Mutane kusan 100 ne suka rasu yayin da wasu mutum 50 suka samu raunuka.
Dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka wasu miyagun 'yan bindiga a jihar Kaduna. 'Yan bindigan dai sun je karbar kudin fansa ne na mutanen da suka sace.
Jagororin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Legas sun ba 'yan Najeriya shawara kan gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Sun bukaci a kara hakuri.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice ya bar jihar a ranar Talata. Gwamnan ya bar jihar ne yayin da rikicin jam'iyyar NNPP mai mulki ya yi kamari.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari