Manyan Labarai A Yau
Mutane masu yawa sun rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a jihar Rivers. Sun yi kira ga gwamnati ta kai musu dauki cikin gaggawa.
Hukumar NBC ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda jami’an hukumar EFCC suka mamaye gidan rediyon Urban FM 94.5 FM a Enugu ana tsaka da watsa shiri.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a jihar Neja inda suka hallaka wasu matafiya mutum uku. 'Yan bindigan sun kuma sace wasu manoma a gonarsu.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake dage taron majalisar zartaswa na kasa (NEC) wanda ta shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Oktoban 2024.
Wasu sojojin saman Najeriya sun gamu da hatsarin mota yayin sa suke kan hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja. Sojoji biyar sun kwanta dama a hatsarin.
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya koka kan rashin shugabanci nagari a kasar nan. Ya ce Najeriya ta kunyata nahiyar Afirika da bakar fata.
Wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a Kano ta umarci 'yan sanda su gudanar da bincike kan zargin lalata da matar aure da ake yi wa kwamishinan Jigawa.
Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya tuna da fursunonin da aka garkame a gidan gyaran hali. Gwamna Ahmed ya yi wa wasu daga cikinsu afuwa.
Gwamnatin tarayya ta bakin ministan tsaro ta bayyana cewa ba za tattauna da 'yan bindiga ba. Ministan ya ce za a ci gaba da fatattakar miyagun a kasar nan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari