Manyan Labarai A Yau
Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare kan kasar Iran a cikin tsakar dare. Iran ta ce hare-haren ba su yi wata barna mai yawa ba yayin da Amurka tace tana sane.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana kan tsuke bakin aljihun gwamnati. Gwamnan ya ce tun bayan hawansa mulki rabin albashi yake karba.
Wata babbar kotun da ke jihar Kano ta ba hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar damar gudanar da zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a jihar.
Peter Obi ya na cikin wadanda suka taya Yakubu Gowon murnar cika shekaru 90 a makon da ya gabata. Sai dai magana a kan Yakubu Gowon ya jawowa Obi matsala a siyasa.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar za ta karbe jihar Rivers. Ganduje ya je jihar Rivers ta APC ce.
Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya yi asarar sama da wayoyin sadarwa 6,000 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023, da suka kai kimanin kudi Naira biliyan 11.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Ndabuisi Mbah ya amince da sabon mafi karancin albashin da zai rika biyan ma'aikatan jihar. Zai fara aiki daga watan Oktoban 2024.
Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ba a kori karamin ministan tsaro ba, Bello Matawalle, duk da zarge-zargen da ake masa.
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne sun kai hari kan wasu mutane a kusa da jami'ar UNIZIƘ a jihar Anambra. Ana fargabar sun hallaka mutane shida.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari