Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata. Gwamnan ya amince da zai biya ma'aikata N75,000 a jihar.
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, ya bayyana yadda ya kwashe shekara uku da rabi a cikin mahaifiyarsa. Amosun ya ce haihuwarsa abin al'ajabi ce.
Mai taimakawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa an sallami Betta Edu daga mukamin minista.
Fadar shugaban kasa ta hannun mai taimakawa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ta ce shugaban kasan yana jin zafin halin da ake ciki.
Wani babban kusa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bukaci 'yan Arewa da su marawa Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima baya a zaben 2027.
Wata kungiya karkashin jam'iyyar APC ta soki korar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Abdullahi T. Gwarzo daga cikin majalisar ministocinsa.
Shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkarim Lawan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sayo sabon jirgin sama ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya soki nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Bianca Ojukuw a matsayin minista. Ya ce siyasa ce kawai.
Kungiyar SERAP ta shigar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu kan bin umarnin da kotu ta ba da.kan zaben 2023.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari