Manyan Labarai A Yau
Sheikh Ibrahim Ahmad Maqary ya soki tsare ƙananan yara saboda zargin cin amanar ƙasa da kifar da gwamnati. Limamin na ganin alkalai da jami’an tsaro sun yi zalunci
Ministar harkokin mata a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ziyarci yaran da aka tsare saboda zanga-zangar da aka yi a watan Agusta.
Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi ta yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kara himma wajen rage radadin da ake ciki.
An shiga jimami bayan rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar Delta, Farfesa Amos Utuama. Marigayin ya rasu ne da safiyar ranar Asabar, 2 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan yaran da aka gurfanar a gaban kotu. Gwamnan ya nuna cewa za su dauki matakin dawo da su zuwa Kano.
Sufeto-Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa sumar da wasu dag cikin yaran da aka gurfanar a gaban kotu suka yi shiri ne kawai.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki matakin gurfanar da kananan yara a gaban kotu da rundunar 'yan sandan Najeriga ta yi a Abuja.
Minista ya umarci ‘yan sanda su sallama takardun sharia da yara masu zanga-zanga. Ministan shari’a, Lateef Fagbemi SAN zai karbi shari'ar yara masu zanga-zanga.
Wasu miyagun 'yan ta'adda sun kai harin ta'addanci a jihar Neja. 'Yan ta'addan sun hallaka 'yan banga 13 a wani kazamin hari karamar hukumar Mariga ta jihar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari