Manyan Labarai A Yau
Za a gudanar da zaben shugaban kasa na kasar Amurka a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamban 2024. Akwai hanyoyin da ake bi wajen bayyana wanda ya yi nasara.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta sakin yaran da aka tsare tare da gurfanar da su a gaban kotu kan zarginsu da hannu a zanga-zanga.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince cewa 'yan Najeriya na fama da tsadar rayuwa a kasar nan. Shugaba Tinubu ya ce matsalar ba Najeriya kadai ta shafa ba.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na kokari wajen ganin an rage tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.
Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana shirin da take da shi na daukar aiki. Gwamna Bala Mohammed, ya bayyana cewa ya shirya daukar mutum 10,000 aiki.
Rikici ya barke tsakanin wani jami'in soja da 'yan sanda a jihar Nasarawa. An samu asarar rayukan mutum biyo bayan barkewar rikicin a ranar Lahadi.
Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta samu kanta a cikin rikici. Wasu 'yan majalisar wakilai guda biyu na jam'iyyar sun fice daga tafiyar Kwankwasiyya.
Matatar Dangote ta yi ƙarin haske kan farashin da take sayarwa 'yan kasuwa man fetur din da ta tace. Ta ce farashinta yafi wanda ake shigowa da shi arha.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun aikata ta'asa a jihar Plateau. Tsagerun sun hallaka surukar dan majalisa tare da dan uwan matarsa. Ya yi alhinin rashin da ya yi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari