Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu tarin yawa. Daga cikin 'yan ta'addan da aka kashe akwai kwamandansu Munzur Ya Audu.
Wasu 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan wani matashin lauya a jihar Benue. 'Yan bindigan sun bi matashin lauyan har gida sannan suka bude masa wuta.
Yan sandan kasar Finland ta kama shugaban yan ta'addar Biyafara, Simon Ekpa. An kama Simon Ekpa ne saboda ingiza mutane su yi ta'addanci a Kudancin Najeriya.
Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa baya tsoron binciken da hukumar EFCC ke yi masa. Ya nuna cewa a shirye yake ya kare kansa.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi alhinin rasuwar Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi. Marigayin ya rasu yana da shekara 93 a duniya.
An samu kuskuren rashin fahimta tsakanin jami'an tsaro na 'yan sanda da 'yan banga a jihar Anambra. Jami'an tsaron sun bude wuta ga junansu a cikin dare.
Hakimin garin Kurfi da ke jihar Katsina, Alhaji Ahmadu Kurfi, ya riga mu gidan gaskiya. Marigayin shi ne tsohon shugaban hukumar FEDECO ya rasu yana da shekara 93.
Hukumar Hisbah a jihar Yobe ta lalata kwalaben barasa da ta cafke a wani aikin sintiri da ta fita. Hisbah ta lalata barasar ne bayan ta kama ta a wani otel.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bukaci a sanya matasa a cikin shirin samar da tsaro a yankin Arewacin Najeriya domin hakan zai taka muhimmiyar rawa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari