Manyan Labarai A Yau
Wani jigo a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya bukaci ka da a tsayar da dan Arewa takara a zaben shugaban kasa na 2027. Ya hango matsala idan aka yi hakan.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa 'yan bindiga sun hallaka wasu daga cikin jami'anta bayan sun yi musayar wuta a jihar Imo. An nemi wani jami'in an rasa.
Mataimakin shugaban majalisar wakilan Najeriya ya tarbi 'yan adawa da suk asauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Abia. Ya yi musu marabar shigowarsu APC.
Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hari kan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda masu yawa tare da lalata makamai masu yawa.
Yunkurin yin tafiye-tafiye ba tare da biza ba a Afirka na karuwa, inda a baya-bayan nan kasashe kamar Rwanda da Kenya suka bude iyakokinsu ga daukacin 'yan Afirka.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi kan rashin da ya yi na wasu daga cikin iyalansa.
Jami'an hukumar DSS sun samu nasarar kai wani harin kwanton bauna a kan tantiran 'yan bindiga a jihar Neja. Jami'an na DSS sun sheke wasu tare da kwato makamai.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi magana kan kuskuren da jami'an tsaro suka yi wajen jefa bama-bamai kan fararen hula a kauyukan Sokoto.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'adda masu kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar nan. Sun hallaka miyagu tare da cafke masu aikata laifuka.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari