Manyan Labarai A Yau
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan ta'addan Lakurawa ne, sun kai hari kan wasu 'yan sanda da ke a shingen bincike a jihar Kebbi. Sun hallaka biyu daga cikinsu.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun bi cikin dare sun yi garkuwa da wasu mutane a jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen ne a cikin dare.
Wata matar aure ta shiga hannun jami'an tsaro bisa zargin hallaka mijinta a jihar Neja. Matar auren ta yi bayanin yadda ta aikata wannan danyen aikin a cikin dare.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya fito ya yabi manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya ce manufofin suna yin aiki sosai.
An samu barkewar rikici tsakanin jami'an tsaro na 'yana banga da mutanen unguwa a jihar Neja. Lamarin ya auku ne bayan an je cafke masu aikata laifi.
Wani tsohon jami'in gwamnatin jihar Kaduna a lokacin Malam Nasir El-Rufai ya shiga hannun jami'an tsaro. Bayan an cafke shi an tura shi gidan kaso.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ware kudade domin biyan basussukan fansho da giratuti na malaman makaranta da suka yi ritaya.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa za a samu ci gaba a kasar nan a shekarar 2025. Ya nuna cewa 'yan Najeriya za su yi murmushi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sako ga gwamnonin jihohin Najeriya kan yancin cin gashin kan kananan hukumomi. Ya kwantar da hankalinsu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari