Manyan Labarai A Yau
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan mutanen da ke garin Gana a jihar Zamfara, 'Yan bindigan sun yi garkuwa da mata da kananan yara.
Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman ya yi martani kan shirin yi masa kiranye da kungiyar dattawan Kaduna (KEF) ta fara. Sanatan yace hakan abin dariya ne.
Wani shaida da komai ya faru a kan idonsa ya bayyana cewa sabon ɗalibi daga Katsin ne ya zo da bom makarantar tsangaya a Abuja, shi da abokinsa sun mutu.
Gwamnan jihar Ondo, Hon. Lucky Aiyedatiwa ya sanar da sa dokar hana fita ta tsawon awanni tun daga safiya har dare a garin Owo, hedkwstar ƙaramar hunumar Owo.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya yi zargin cewa ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sukar da yake yi wa gwamnatin Bola Tinubu.
Masarautar Ilorin ta musanta rahoton da aka fara yaɗawa cewa sarki Sulu Gambari da Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara sun fara zaman doya da manja.
Bidiyon Faston Cocin Angelican a otel tare da budurwa ya tada cece-kuce a Kenya, inda ake zargin an hada baki don kamashi da neman kudi da bidiyon.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sababbin kwamishinonin da ya nada a gwamnatinsa. Gwamnan ya kuma rantsar da masu ba da shawara.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun taso mutanen wasu kauyukan jihar Zamfara a gaba. Tsagerun 'yan bindigan sun sanya harajin N172m kan kauyukan da ke Tsafe.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari