Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar NNPP mai adawa ta harzuka kan kalaman da Nasir El-Rufai ya yi na cewa gwamnatin tarayya na da hannu a cikin rikicin da ya addabe ta. Ta ba shi wa'adi.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya fito ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana shirin barin APC domin komawa jam'iyyar SDP. Ya ce karya ce tsantsagwaronta.
Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewa 'yan majalisar dokokin jihar na da hurumin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dauko matasa ya ba su mukamai a cikin gwamnatinsa. Gwamna Mai Mala Buni ya nada matasa 200 a matsayin hadimansa.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani mummunan harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Zamfara. Sojojin sun hallaka miyagu masu tarin yawa.
Wasu 'yan ta'adda da ake zargin na Boko Haram ne sun kai harin ta'addanci a jihar Yobe. 'Yan ta'addan sun hallaka wani dan sa-kai tare da kona gidaje.
Kotun kolin Najeriya ta shirya yanke hukunci kan taƙaddamar da aka jima ana yi game da batun mayar da Al-Mustapha Jokolo kan kujerar sarkin Gwandu.
Gwamnan jihar Jigawa ya kai ziyarar gani da ido kan yadda shirin raba abinci na watan azumin Ramadan ke guduwa. Gwamnan ya nuna damuwa kan abin da ya gani.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi zargin cewa jam'iyyar APC da gwamnati mai ci na da hannu a rikicen da suka addabi jam'iyyun adawa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari