Manyan Labarai A Yau
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bai sanya batun zaben 2027 a gabansa ba. Ta ce ya damu kan yadda zai inganta rayuwar jama'a.
Tsohon ministan sadarwa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana cewa ya ki yarda da wani tsarin da ake amfani da shi a gwamnati, saboda bai yadda da halascinsa ba
Gwamnatin sojin Nijar karkashin Tchiani ta nemi taimakon gwamnatin Najeriya bayan karancin fetur ya kusa tsayar da lamura cak. Bola Tinubu ya ba su tankar mai 300.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana kudaden fansan da 'yan bindiga suka nema kan matashin mahaddacin Al-Kur'anin da suka sace a kwanakin baya a jihar.
Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmad Aliyu ta shirya karya farashin kayan abinci. Gwamnatin ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasarar dakile wani harin ta'addanci da 'yan bindiga suka yi kokarin kai wa a jihar Zamfara.
Kwamitin ladabtarwa zai saurari shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti kan zargin cin zarafi, sanatoci da dama za su ba ds shaida.
Jam'iyyar SDP ta yi sabon zargi kan gwamnatin APC mai mulki a Najeriya. Ta ƴi zargin cewa ana shirin sanya tsoro a zukakan 'yan adawa tare da barazana a gare su.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun tursasa mutane zuwa cikin daji.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari