Manyan Labarai A Yau
Dakarun sojojin Najeriya sun kai hare-hare kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. Hare-haren sun yi sanadiyyar hallaka mayaka da kwamandojin kungiyar.
Tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta mutu murus. Ya nuna cewa APC ce ke juya ta.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na da dabi'ar tafiya zuwa yin hutu a kasashen waje tun bayan hawansa mulki. Shugaban kasan ya kwashe kwanaki yana hutu.
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyara kabarin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Daura, inda 'yan Najeriya suka yi martani gan sauyin da suka gani.
Wani rahoto ya nuna cewa Jamus, Ostiraliya, da Portugal sun zama wurare masu sauƙi kuma masu araha ga 'yan Najeriya da ke neman ƙaura, a maimakon Amurka da UK.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai karar kwamishinan ’yan sanda da wasu jami’ai ga hukumar PSC, yana zarginsu da saba doka da karya ka’idojin aikin su.
Dakarun sojojin Najeriha sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a jihar Katsina bayan sun yi artabu. Sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutanen da aka sace.
An tabbatar da mutuwar matar nan da ta bai wa ilimi gudummuwa a Najeriya kuma mai rike da sarautar Yeye Mofin ta Legas, Leila Fowler a jiya Lahadi, 7 ga Satumba.
Tsohon ministan wasanni a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya ba da tabbacin cewa jam'iyyar ADC ta shirya kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari