Manyan Labarai A Yau
Majalisar sarakunan Idoma da ke jihar Benue ta bayyana cewa babu inda ta ce ta soke sarautar da aka bai wa shugaban kasa, Bola Tinubu da sakataren gwamnatinsa.
Tushen wutar lantarki na ƙasa ya sake rushewa a Najeriya, ya rage wuta zuwa 50MW kacal ga DisCos. AEDC ta tabbatar da lamarin, miliyoyin jama’a sun shiga duhu.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile harin 'yan bindiga a jihar Katsina. Sojojin sun samu nasarar ne tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa taro ya tarwatse tun kafin a gaba a jihar Osun bayan an bukaci rubuta takarda ga Gwamna Adeleke da nufin karbe rawanin Sarkin Ipetumodu.
Madugun tafiyar Kwankwasiyya kuma jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ganawa ta musamman da jagororin jam'iyyar a Cross River.
Dakarun sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara. A yayin artabun an kashe 'yan bindiga masu yawa yayin da aka samu asarar rayukan wasu sojoji.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun kashe mutane tare da yin awon gaba da wasu masu yawa.
Wata kungiyar dattawan Arewa ta shawarci gwamnonin yankin da su bi hanyar sulhu domin kawo karshen matsalar rashin tsaro. Ta ce sulhu abu ne mai kyau.
Wani matashi ya yi tattaki daga Ikorodu zuwa Abakaliki na tsawon kwanaki 17 don godiya ga Gwamna Nwifuru, ya samu kyaututtuka ciki har da tallafin N10m.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari