Manyan Labarai A Yau
Mai martaba sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya naɗa Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano a gaban Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan jihar Neja, Muhammed Umaru Bago ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa ba ya ga maciji da mataimakinsa, Yakubu Garba, ya ce kansu a haɗe yake.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya musanta zargin cewa hukumar tana muzgunawa 'yan adawa a Najeriya.
Hadimin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, Lere Olayinka, ya bayyana cewa hadakar da Alhaji Atiku Abubakar ke jagoranta ta mutu murus.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mace mafi tsufa a duniya, Inah Canabarro Lucas ta rasu ta na da shekarƴ 116 a duniya, an tabbatar da mutuwarta ranar Larava.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya miƙa sakok ta'aziyya ga abokiyar aikinsa, Dr. Mariya Mahmoud bisa rasuwar mahaifinta, Alhaji Sani Baban Koko.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan binciken tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi kira ga gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, da ya sake tunani kan shirinsa na sauya sheka zuwa wata jam'iyyar.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi bayani kan yadda Nyesom Wike ya jawo Peter Obi ya fice daga PDP kafin zaben 2023.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari