Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Anambra ta kammala shirin tallafawa matasa 8,300 da kuɗi N3.5bn a ƙarƙashin shirin '1Youth2Skills Plus' domin taimaka musu su fara kasuwanci.
Wani kusa a jam'iyyar APC ta jihar Kaduna, ya yabawa Gwamna Uba Sani, ya bayyana cewa ko kadan ba ya barci don neman sauke nauyin da aka dora masa.
Babban jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa za a iya samun rikici a kasar nan, idan har aka nada wani tsohon alkali a matsayin shugaban INEC.
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Pantami ya karbi bakuncin dan takarar LP a zaben shugaban kasar 2023, Peter Obi a birnin Abuja.
Wata kotu ta musamman da ke zamanta a jihar Legas, ta amince da bukatar da tsohon babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya gabatar a gabanta.
Wani kusa a jam'iyyar APC ta jihar Kano, Jadda Garko, ya yi zargin cewa an shirya masa zagon kasa don ka da ya samu mukami a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Babban kusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na kokarin tarwatsa 'yan adawa. Ya ce ba za ta yi sahihin zabe ba.
Fadar shugaban kasa ta fito ta tanka kan sukar da Atiku Abubakar ya yi na cewa ta kasa magance matsalar yunwa da talauci. Ta ce tana alfahari da ci gaban da ta samu.
'Yan sanda sun samu raunuka daban-daban yayin da hatsarin mota ya rutsada ayarin shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt Hon. Haruna Aliyu Dangyatin.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari