Manyan Labarai A Yau
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka jami'an tsaro na rundunar Askarawan Zamfara. Sun kuma yi awon gaba da makamai daga hannun jami'an tsaro.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa ta cafke wani kasurgumin hatsabibiɓ dan bindiga da jami'an tsaro suka kwashe shekara 11 suna nema.
An shiga alhini a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano lokacin da wasu matasa suka faɗa magudanar ruwa da aka toshe, an rasa rayuka huɗu a ibtila'in.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ziyarar da ya kawo saboda rasuwar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata.
'Yan binduga da ke dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun sace dabbobi masu yawa tare da raunata wasu mutane a yayin harin.
Tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana cewa Buhari na son ministocinsa kamar yadda yake kaunar talakawa.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gamu da koma baya a jihar Osun. Daga daga cikin sanatocinta da ke majalisar dattawa ya yi murabus daga cikinta nan take.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauka a filinin jirgin sama na Malam Aminu Kano domin zuwa ta'aziyya gidan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata yau Juma'a.
Tsohon ɗan takarar ADC, Dumebi Ƙachikwu ya bayyana cewa tun a baya, Atiku Abubakar ba ya ƙaunar ɗan Kudu ya karɓi shugabancin Najeriya, ya ce tun 2003.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari