Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Ebonti ta hannu mai dakin Gwamna Francis Nwifuru ta fara rabawa zawarawa tallafin gidaje domin su samu wurin zama a kananan hukumomi 13.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da wani basarake tare da wasu mata zuwa cikin daji.
Gwamnatin jihar Kano ta bukaci mutane su kiyaye matakan lafiya domin gujewa kamuwa da zazzabi mai tsanani da ke sa zubar da jini, ta fitar da matakai uku.
Wani babban turken wutar lantarki ya ruguje a Rigasa, karamar hukumar Igabi, lamarin da ya jefa dubban jama’a a Kaduna cikin duhu, sakamakon iska da ruwan sama.
Wasu masu ruwa da tsaki a APC ta jihar Enugu sun bayyana damuwarsu kan yadda wasu jagorori ke neman toshe lafar sauya shekar gwamna Peter Mbah zuwa APC.
An yada wata jita-jita mai cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya fice daga jam'iyyar. Shugaban APC a karamar hukumarsa ya yi bayani.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihar Benue. Ana fargabar cewa an hallaka sama da jami'ai guda 10.
Kasashen Birtaniya, Canada da Austalia sun bi sahun masu amince da kafa kasar Falasdinu. Ana sa ran wasu kasashe za su bi bayansu a taron majalisar dinkin duniya.
Kungiyar APC North Central Forum ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi kaffa-kaffa da wasu gwamnonin jam'iyyun adawa kan zargin muzgunawa 'yan APC.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari