Manyan Labarai A Yau
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kira ga 'yan siyasa da su dauki dabi'un yafiya da hakuri. Jonathan ya ce bai taba rike kowa a zuciyarsa ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya hada kai da kasashen duniya da suka fara kiraye-kirayen a bai Falasdinawa damar kafa kasar Faladinu don kawo karshen rikici.
Hukumar NUC ta yi gargadi ga dalibai yayin da ta fitar da sunayen jami’o’in bogi 58 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a fadin Najeriya, suna ba da digiri marasa inganci.
Sanata Nelson Effiong, wanda ya wakilci Akwa Ibom ta Kudu daga 2015 zuwa 2019 ya zama Magajin Gari a kauyensu, ya ce lokaci ya yi da za su bar harkar siyasa.
Shugaban hukumar EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya, Ola Olukoyede, ya nuna muhimmanxin hadin kai a yakin da ake yi kan masu aikata laifuffuka.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kwara. 'Yan bindigan sun hallaka jami'in dan sanda tare da yin awon gaba da wasu.
Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera, ya kai zuciya nesa bayan ya sha kaye a zabe. Ya dauki waya ya kira abokin hamayyarsa don taya shi murna.
Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ya sallami wasu manyan jami'ai biyu daga aiki bisa laifin amfani da takardun bogi.
Hukumar binciken hadurra ta NSIB ta gano cewa rashin ingantaccen gyara da matsalar na'ura ne suka haddasa hatsarin jirgin kasa a tashar, hanyar Abuja–Kaduna.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari