Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya rasa daya daga cikin hadimansa. Gwamnan ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin wanda ya rasu.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar cafke wasu mutane da ke hada baki da 'yan bindiga. An cafke mutanen ne suna kokarin kai man fetur ga miyagu.
An yi rashi a jihar Bauchi bayan rasuwar daya daga cikin shugabannin kananan hukumomi. Gwamna Bala Mohammed ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin.
An shiga jimami a jihar Zamfara bayan wani ramin hakar ma'adanai ya rufta da mutane. Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon aukuwar lamarin.
Kungiyar Obedient Movement ta bayyana cewa Peter Obi ba ya gaggawar son zama shugaban kasa, kuma sai ya yi shawarwari sosai kafin sauya jam'iyya.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya kan matsin tattalin arziki. Ya ce an sha wahala ne saboda matakan da gwamnatinsa ta dauka masu tsauri.
Olubadan na 44 da ya hau kan sarauta, Oba Rashidi Ladoja ya roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kirkiro jihar Ibadab kafin zaben 2027.
Bayan watanni uku da rasuwar Olubadan na 43, tsohon gwamnan jihar Osun, Rashidi Ladoja ya dare karagar Sarkin kasar Ibadan na 44 yau Juma'a a jihar Osun.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa mutanen Kano za su goyi bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari