Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ba gwamnonin Arewa shawara kan matsalar rashin tsaro. Gwamnan ya bukaci su tashi tsaye wajen magance matsalar.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin suna hada baki da 'yan ta'adda a jihar Katsina. Sojojin sun kuma kubutar da wani mutum.
Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta yi barazanar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani. Ta ba gwamnati wa'adi don ta biya mata bukatun da ta dade tana nema.
Hukumar Jin Dadin 'Yan Sandan Najeriya (PSC) ta kara rasa daya daga cikin tsofaffin shugabanninta, DIG Perry Osayande, wanda ya rasu a Benin, jihar Edo.
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun 'yancin kai.
Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasa (PENGASSAN), ta tsudunma yajin aiki a fadin Najeriya. Lamarin ya kawo tsaiko a kamfanin NNPCL da NUPRC.
Tsohon ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Farfesa Jerry Gana, ya ba da tabbacin cewa Goodluck Jonathan, zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kalaman zargi kan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ya nuna cewa bai san yadda ake gudanar da mulki ba.
'Yan bindiga sun kai farmaki a garin Dabai da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun fuskanci tirjiya daga wajen jami'an tsaro da 'yan sa-kai.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari