Manyan Labarai A Yau
Yara hudu sun jikkata da wata kwalbar barkonom tsohuwa mai sanya hawaye ta fashe a Sharada da ke cikin birnin Kano, yan sanda sun gudanar da bincike kan lamarin.
Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya fito ya yi magana kan wasu rahotannin da ke cewa zai hakura da takara a zaben 2027.
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), ya tabo batun illar da yajin aikin kungiyar manyan ma'aikatan man fetur na kasa (PENGASSAN) ya jawo a kasa.
Tsofaffin tsagerun Neja Delta sun nuna goyon bayansu ga tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027. Sun bayyana cewa Tinubu ya yi abin a zo a gani.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimmin kira ga 'yan Najeriya. Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su daina yin kalamai marasa kyau a kan kasar.
Gobara da ta tashi a kasuwar Bariga da ke jihar Legas ta jawo asarar miliyoyin Naira a safiyar ranar Laraba. Hukumar LASEMA ta ce shaguna 26 suka kone.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kai ziyarar gani da ido kan yadda aikin gina wani titi yake tafiya a Kaduna. Gwamnan ya ce za a kammala aikin cikin watanni tara.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ga gayawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa akwai wasu karin gwamnonin adawa da za su dawo APC.
Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutane 26 a hatsarin jirgin ruwan da ya rutsa da yan kasuwa ranar Litinin, Gwamna Ahmed Ododo ya yi ta'aziyya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari