Manyan Labarai A Yau
Sarkin Kirawa ya tsere zuwa Kamaru bayan Boko Haram sun kai hari suka ƙone fadarsa, suka kashe mutane biyu, yayin da dubban jama’a suka gudu daga Gwoza.
Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bukaci kungiyar Hamas ta saki mutanen Isra'ila da ke hannunta ba tare da sharadi ba, ya ce tun farko an yi kuskure.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar dakatarwar da majalisa ta yi wa Sanata Natasha.
Bayan jin cewa Rarara ya samu digirin girmamawa daga jami'ar European-American, Legit Hausa ta zakulo mawaƙan Hausa 5 da suka taɓa samun irin wannan karramawa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a jihar Kwara. 'Yan bindigan sun kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu da dama. An kuma kona gidaje.
Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Remi Tinubu, ta bayyana cewa ta shiga cikin wani lokaci lokacin zaben shekarar. Ta ce an ci amanarta a inda ba ta yi zato ba.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dauko dan marigayi Bukae Abba Ibrahim, mukami a gwamnatinsa. Gwamnan ya nada shi matsayin mai ba shi shawara.
Matatar Dangote ta yi tayin biyan albashi ga ma'aikatan da ta kora saboda zargin cin amana. Sai dai kungiyar PENGASSAN ta ki amimcewa da bukatar matatar.
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan rikicin Boko Haram. Ya bayyana cewa ya kamata a dauki kwararan matakai don magance matsalar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari