Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi tsokaci kan zargin da ake yi wa minista a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kan yin amfani da takardun bogi.
Jirgin British Airways ya yi gaggawar sauka a Barcelona ta lsar Spain byan wani babban soja mai ritaya ya rasu ana cikin zuwa birnin Abuja a Najeriya.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, zai yi rabon tallafi ga marasa galihu a jihar Kano. Za a raba tallafin ne dukkan kananan hukumomi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala ziyarar da ya je yi a jihar Legas. Shugaban kasa ya tattaro kayansa ya dawo babban birnin tarayya Abuja.
Ministan Kimiyya da Fasaha da ake zargi da amfani da takardun digiri da NYSC na bogi, Uche Nnaji ya shirya fitowa bainar jama'a domin kare kansa.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole, ya ja kunnen tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan yin takarar a babban zaben shekarar 2027.
Imisi ta lashe BBNaija zango na 10 da 42.8% na kuri’u, ta tafi da kyautar Naira miliyan 150, mafi girma a tarihin shirin, bayan makonni 10 ana fafatawa.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta ragargaji shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ta nuna cewa shugaban kasan yana yi wa rashin tsaro rikon sakainar kashi.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a jihar Neja. 'Yan bindigan sun hallaka wani shugaban 'yan sa-kai tare da yin garkuwa da wasu mutane.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari