Manyan Labarai A Yau
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya nuna damuwarsa kan sauya shekar da wasu ke yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Ya ce ya damu matuka sosai.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da yi wa mutane 175 afuwa cikinsu har da wadanda aka yanke wa hukuncin kisa, Maryam Sanda za ta koma cikin iyalanta.
Jami'an Tsaron filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas sun cafke wasu matasa dauke da kudi tsaba, sama da Dalar Amurka biliyan 6.1.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci Majalisar Dokokin Jihar Benuwai, ta sake nazari kan batun bashin da Gwamna Alia zai karbo har Naira biliyan 100.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda tare da kwato kudade masu kauri a hannunsu.
Jam'iyyar LP mai adawa a Najeriya ta bukaci Alhaji Atiku Abubakar ya goyawa Peter Obi baya a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar IIl, ya bukaci gwamnonin Arewa au tashi tsaye don kawo ci gaba a yankin. Ya bukaci su yi aiki tukuru.
'Yan bindiga dauke da makamai sun yi wa jami'an 'yan sa-kai na CJTF kwanton bauna a jihar Zamfara. Miyagun sun hallaka jami'an tsaron a artabun da aka yi.
Tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. An gano dalilinsa na yin hakan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari