Manyan Labarai A Yau
Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi magana kan halin da ya tsinci kansa a cikin a zaman da ya yi a gidan yari. Ya bayyana cewa ya koyi darussa sosai.
Tsohon ministan wasanni kuma shugaban kungiyar MEN, Solomon Dalung ya yi kiran da aka saki DCP Abba Kyari. Ya bayyana cewa ci gaba da tsare shi ba adalci ba ne.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan yajin aikin kungiyar ASUU. Ta bukaci shugabannin jami'o'i su rike albashin mambobin kungiyar.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bukaci mambobin jam'iyyar PDP da kada su karaya kan yawan ficewar da wasu ke yi. Ya ce jam'iyyar za ta farfado.
Wani kusa a jam'iyyar APC mai mulki, Khamis Darazo, ya nuna damuwa.kan yiwuwar ficewar tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami daga jam'iyyar.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya tabo batun matsalar rashin tsaro. Ya bayyana cewa dole sai gwamnati ta magance yunwa kafin a shawo kan matsalar.
Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya yi kari kan farashin litar man fetur. Kamfanin ya yi karin ne a gidajen man da ke a biranen Abuja da Legas.
Gwamnatin jihar Kebbi ta musanta batun cewa 'yan bindiga sun kai kazamin hari a jihar. Ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin rahotannin kai harin.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi afuwa ga wasu 'yan Najeriya da aka yankewa hukunci. Daga cikinsu har da wadanda aka yi wa ragin zaman gidan yari.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari