Manyan Labarai A Yau
NiMet ta gargadi jihohin Najeriya 20, ciki har da Sokoto da ke cikin matsanancin haɗari, game da ambaliyar ruwa a Yuli, tare da ba da shawarwarin kariya.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta nuna danuwa kan yadda aka yi fada a fadar Sarki Muhammadu Sanusi duk da akwai jami'an tsaro.
Masarautar Kano ƙarkashin jagorancin Muhammadu Sanusi II ta zargi Magoya bayam Aminu Ado Bayero da kai hari fadar Kofar Kudu, inda suka lalata kofar shiga.
An tsinci gawar Starovoit, ministan harkokin sufurin Rasha, da harbin kansa a kusa da Moscow, bayan korarsa daga aiki da kuma zargi da hannu a badakalar Kursk.
Wasu mambobin ADC uku sun kai kara gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja, sun ƙalubalanci naɗin shugabannin rikon kwarya da aka yi kwanan nan.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana cewa ba ta da wata fargaba kan hadakar 'yan adawa da ke son kawo karshen mulkin Tinubu a shekarar 2027.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ba ruwamta da duk wani abu da ya shafi ƙera makaman nukiliya.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Ya ce zai fadi jam'iyyar da zai koma.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ce kamar yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya faɗa kwanakin baya, sun jin tsoron Gwamna Peter Mbah.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari