Manyan Labarai A Yau
Wannan rahoto ya duba muhimman gudunmawar da za a ci gaba da tunawa da su a game da Dantata — daga ilimi da lafiya zuwa taimakon gaggawa, addini da ci gaban al’umma
Gwamna Abba Yusuf ya naɗa ƙarin manyan masu taimaka masa na musamman guda 19 don ƙarfafa shugabanci tare da fatan za su ba da gudunmawa ga ci gaban Kano.
Fulani a Bauchi sun ƙi amincewa da sababbin masarautun da Gwamna Bala Mohammed yake son kirkirowa, sun ce sun fi son bin tsofaffin masarautun jihar 6.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa idan ya samu damar zama shugaban ƙasa a 2027, zai yi sheksra huɗu ne kaɗai don mutunta tsarin karɓa karɓa.
Sabon rikici ya ɓarke a Lamurde da Guyuk a jihar Adamawa, inda gidaje biyu suka ƙone, rundunar ‘yan sanda ta fara bincike tare da tura jami’an tsaro yankin.
Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ya zama dole lauyoyi su koyi amfani da fasahar zamani idan suka son aikinsu ya tsira.
G-7 ta goyi bayan Isra'ila yayin da ta kira Iran da zama tushen duk rikicin da ke faruwa a Gabas Ta Tsakiya. G-7 ta ce ba za ta yarda Iran ta mallaki nukiliya ba.
Kakakin majalisar Filato ya yi murabus, an zaɓi Nanloong Daniel na APC, yayin da ake sa ran hakan zai dawo da zaman lafiya bayan rikicin siyasa a jihar.
Yan kasuwa sun ki su rage farashin litar man fetur a gidajen mansu duk da matatar Ɗantoge ta yi rangwamen N40, sun ce suna da tsohon kaya da suka saya da tsada.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari