Manyan Labarai A Yau
An tabbatar da rasuwar tsohon dan takarar gwamnan jihar Ondo karkashin inuwar jam'iyyar SDP, Otunba Bamidele Akingboye a gidansa da ke jihar Legas.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin 'yan kungiyar Buhari a fadarsa da ke Abuja. Ya gaya musu cewa ba zai iya nada kowa a kan mukami ba.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar LP a 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya taso Nasir El-Rufai a gaba kan zargin da ya yi wa gwamnatin Bola Tinubu.
Wata Kotun Majistare a jihar Ebonyi ta bayar da umarnin a tsare wani malamin addini bisa zargin yunkurin kisan kai, haddasa gobara, da sauran laifuffuka.
Jigo a jam'iyyar APC a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya caccaki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, bayan ya yi kalaman zargi kan gwamnatin Bola Tinubu.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Kogi. 'Yan bindiga sun sace basaraken ne lokacin da yake kan hanyar dawowa daga taro.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a sake duba ayyukan samae da tsaro a jihar Katsina. Ya umarci a kara sayo kayan aiki ga jami'an tsaro.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Datti Baba Ahmed, ya bayyana cewa ya kamata hukumomi sun binciki Nasir El-Rufai.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, ya bayyana yadda 'yan daba suka kaiwa tawagarsa farmaki bayan ya dawo daga fadar sarki wajen yin ta'aziyya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari