Manyan Labarai A Yau
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa, EFCC ta fara neman shugaban wani kamfani, Ogundele, ruwa a jallo kan zargin almundahana da karakatar da kudi.
NiMet ta yi hasashen iska mai karfi tare da ruwan sama a Arewa, da Kudancin Najeriya a ranar Juma’a, ta gargadi al’umma da su zama cikin shirin ambaliya.
Kwamishinan hukumar da'ar ma'aikata kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, Hon. E.J. Agbonayinma ya karyata labarin cewa guba aka sanya wa Arase a abinci.
Gwamnonin Arewa maso Gabas sun mika jerin bukatunsu na tsaro da ababen more rayuwa ga shugaba Tinubu don tallafawa ci gaban yankin. Tinubu ya kwantar da hankulansu.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna matukar bacin ransa bayan 'yan sanda sun kawo cikas ga shirin shugabannin ASC na gudanar da taro.
Jagoran 'yan bindiga a jihar Zamfara, ya fusata inda ya bindige wasu daga cikin mayakansa. Ado Aleiro ya yi kisan ne da kansa kan zargin cin amana.
An tabbatar da mutuwar akalla mutane 60 bayan wani jirgin ruwa ya juye mutane kusan 100 a teku, galibin wadanda ke cikin jirgin mata ne da kananan yara.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya koka kan matsalar rashin tsarom da ake fama da ita. Ya nuna cewa yana da masaniya kan shugabannin 'yan bindiga.
Wasu mutanen gari sun cire tsoro sun yi arangama da 'yan bindiga a jihar Sokoto. A yayin arangamar an ceto mutanem da aka sace tare da kashe 'yan bindiga.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari