Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Kebbi karkaahin jagorancin, Gwamna Nasir Idris, ta yi zargin cewa an janye dakarun sojoji kafin 'yan bindiga su sace dalibai zuwa daji.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi da kansa ya je Amurka domin ganawa da Donald Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sanya ya daina shiga harkokin siyasa tun bayan barinsa kan mulki.
Mai ba shigaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya gana da sakataren tsaron Amurka da shugaban hafsoshin tsaro kan baranazar Donald Trump.
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Uzor Orji Kalu, ya bayyana cewa akwai dalilin da ya sanya Mai girma Bola Tinubu bai je jihar Kebbi ba.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto. Miyagun sun hallaka mutane tare da sace iyaye mata da jariran da suke shayarwa.
Babbar kotun tarayya ta yanke wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, hukuncin daurin rai-da-rai tare da wasu shekaru 25 a gidan yari. An sanya matakan tsaro masu tsauri.
Jam'iyyar ADC ta sake samun kanta a cikin wani rikici. Tsagin jam'iyyar ya zargi Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran 'yan hadaka da yunkurin kwace jam'iyyar.
Gwamnatin jihar Zamfara ta hannun hukumar Zakka da Wakafi ta shirya gudanar da auren gata ga wasu marayu a jihar. Za kuma ta bada tallafi yin sana'o'i.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari